Daular Duguwa

Daular Duguwa
dynasty (en) Fassara

Daular Duguwa, ko Dougouwa shekarar (700-1086), ita ce daular sarakunan ( mai ) na Daular Kanem kafin hawan daular Seyfawa ta Musulunci a shekarar 1086.[1]:21

A cewar Girgam, sarakunan Duguwa su ne sarakunan Kanem waɗanda sunansu na sarauta ya samo asali ddaga Duku, sarki na uku na Duguwa. Kwatanta bayanan da masanan Larabawa suka yi ya nuna cewa Duguwa sune sarkan masu mulki da ake kira Zaghawa. Har zuwa kwanan nan masana tarihi sun yi imanin cewa sarakunan Duguwa da aka ambata a cikin Girgam sun yi sarauta a Kanem kafin sarakunan Musulmi na farko.[2]

Richmond Palmer ya ce, "Ga dukkan alamu duka labaran Saif ibn Dthi Yazan da dansa Ibrahim tatsuniya ce. Mai Kanem na farko shi ne 'Mai Dugu Bremmi,' wanda ya yi nasara saboda shi ne 'dugu' ( tegasi ) ko dan 'yar sarki ko 'yar'uwarsa..." "Sunan dugu yana nufin tsantsan cewa shi ɗan 'ya ne ko Mai, ko kuma babban sarki, watau mutumin da Abzinawa ke kira tegasi, ko magaji." "Tsarin Maghumi, kamar yadda yake a cikin Abzinawa, ya wuce ga ɗan 'yar'uwar sarki ,marigayin, wanda ake kira a cikin Abzinawa, tegasi ko magaji..." "A yadda Tsarin kakanin Saifawa yazo , kamar yadda ake kira Maghumi., kawai ya zama a zamanin Musulmi Saif, 'Zakin Yaman'."[3]

Wani masanin tarihi ya nuna cewa duka sarakunan Duguwa banda ɗaya daga cikin, U kasance tsoffin sarakunan Gabas ne. Sunayensu da mukamansu sun shaida kafa Kanem da 'yan gudun hijira daga Daular Assuriya suka yi a c. 600 BCE.[4] Wannan hasashe, duk da haka, ba a yarda da shi ba.

  1. Cite error: Invalid <ref> tag; no text was provided for refs named Urvoy
  2. Smith: Early states, 167.
  3. Palmer, Richmond (1936). The Bornu Sahara and Sudan. London: John Murray. pp. 9, 38, 118, 180.
  4. Lange: Founding of Kanem, 13–18.

From Wikipedia, the free encyclopedia · View on Wikipedia

Developed by Tubidy